IQNA

An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)

23:45 - May 29, 2017
Lambar Labari: 3481561
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da karatun hatmar kur’ani da ake gudanarwa a kowacea cikin watan Ramadan mai alfarma a hubbaren Hussaini (AS) da ke Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama’a na cibiyar Darul kr’ani da ke kula da harkokin kur’ani a hubbaren Imam Hussain (AS) ya sanar da fara karatun hatma da ake yi a kowace a daidai wannan lokaci a cikin hubbaren mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an fara wannan hartma tare da karatun izihi biyu a kowace rana, wanda kuma za a kammala a daren karshe na watan Ramadan mai alfarma.

Wannan karatu dai ya kunshi bangarori biyu kamar yadda aka saba, akwai bangaren mata, wanda suke gudanar da nasu karatu a wani bangare na musamman da ke cikin wannan hubbare, akwai kuma bangaren maza wanda shi ne yafi yawa.

Baya ga karatun kur’ani kuma ana gabatar da jawabai da suka danganci darussan da wannan littafi mai tsarki yake koyar da musulmi, wadanda manzon Allah ya koyar da su a aikace a cikin rayuwarsa mai albarka.

Hatmar Kur’ani A Hubbaren Alawi

Bangaren yada labarai na cibiyar kur’ani ta Darul Kur’ani da ke can hubbaren Imam Ali (AS) a birnin Najf ma ana gudanar da wani karatun na hatma makamancin wannan, wanda ya kebanci mata da kuma kanan yara.

Safa Mahdi Al-amiri daya ce daga cikin malaman kur’ani da suke kula da wannan karatu na hatma ta bayyana cewa, karatun da ake yi a wannan hubbaren wani bangare ne da yakebanci mata da kuma yara ‘yan kasa da shekaru 17 kamar yadda aka saba.

3604405


An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)

An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)

An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)

An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)

An Fara Karatun Hatma A Hubbaren Imam Hussain (AS)
captcha