Mahyush Ayyub ita ce shugabar wannan cibiya, ta bayyana cewa bababr manufarsu ta ce yada al'adun muslunci da kuma wayar da kan mata msuulmi, musamman ganin irin yadda kyamar musulmi ke karuwa a kasar, inda mata kuma su ne suka fi shiga matsala.
Daga cikin ayyukan da cibiyar za ta yi har da amsa tambayoyi da bayar da shawarwari ga mata kan lamurra na zamantakewa da kuma sanin halin da suke ciki da abubuwan da suke faruwa da su, domin kai musu dauki a lokacin da suka ga za a cutar da su.
Cibiyar ta yi rijista tare da sanar da jami'an tsaro dukkanin ayyukanta, inda mahukunta a kasar ta Canada suka nuna amincewarsu da hakan, a kan haka jami'an tsaro da na gwamnati za sy rika bayar da hadin kai ga wannan cibiyar domin ayyukanta su yinasara.