IQNA

Rasha Ta Ce Akwai Yiwuwar An Kashe Albaghdadi

23:54 - June 16, 2017
Lambar Labari: 3481616
Bangaren kasa da kasa, ma’ikatar harkokin wajen Rasha ta ce akwai yiwuwar an kasha jagoran ‘yan ta’addan ISIs Abubakar Baghdadi a wani hari a kusa da Raqqa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran shafaqana cewa, ma’aikatar tsarin kasar rasha ta ce akwai yuwar an halaka jagoran kungiyar ‘yan ta’adda ta daesh Abubakar Baghdadi a wani hari da aka kai a kusa da Raqqa.

Bayanin ya ce a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata, Rasha ta kai wani hari da jirgi maras matuki a wani wuri a kusa da birnin raqqa da ke hannun ‘yan ta’addan takfiriyyah na ISIS, bayan samun bayanai a kan cewa wasu gungun ‘yan ta’addan suna gudanar da wani zama.

Ma’aikatar tsaron ta Rasha ta ce ‘yan ta’addan suna tattaunawa akan shirin ficewa da Raqqa, inda jirgin na Rasha ya tarwatsa wurin da suke gudanar da zaman, an kuma kasha mayakan ISIS 330 a wurin, da suka hada har da manyan kwamandojin kungiyar guda 30 da ake kyautata zaton cewa hart da Abubakar Baghdadi a cikinsu.

Rasha ta ce ta samu cikakken bayani kan fin ‘yan ta’addan su taru a wurin da kuma lokacin da za su taru da kuma abin za su tattauna a kai, kuma daga cikin wadanda za su halarci wurin har da Abubakar Baghdadi, wanda kuma mafi yawan wadanda suka halarci wurin daga cikin ‘yan ta’addan sun halaka sakamakon harin na Rasha.

A nata bangaren Amurka ta bayyana cewa ba za ta yi saurin amincewa da wannan bayani na Rasha dangane da halaka Abubakar Baghdadi ba.

3610127


captcha