IQNA

An Kai Harin Bam A Kan wata Cibiyar Kur'ani Syria

17:19 - July 05, 2017
Lambar Labari: 3481673
Bangaren kasa da kasa, Wasu 'yan ta'adda sun kaddamar da harin bam a kan wata cibiyar koyar da kor'ani mai tsarki a garin Qunaitra da ke cikin gundumar Idlib a kasar Syria, tare da kashe mutane 7 da jikkata wasu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shfain yada labarai na Almuslim ya bayar da rahoton cewa, 'yan ta'addan sun tayar da wata mota da suka shakare da bama-bamai a kusa da ginin cibiyar, inda suka kashe fararen hula akalla 7 tare da jikkata wasu da dama.

Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun ajiye mitar ne kuma suka tayar da ita daga nesa, wanda hakan ya rusa mafi yawan bangarorin ginin cibiyar.

Babu wata kungiya dagta cikin kungiyoyin 'yan ta'addan na Syria da ta dauki alhakin kai harin, amma dai ana dora alhakin hakan a kan kungiyar 'yan ta'addan wahabiyya takfiriyya ta Jabhat Nusra, wadda take samun dauki daga Isra'ila gami da Saudiyya da kuma Amurka da Turkiya.

3615656


captcha