IQNA

An Fara Watsa Shirin Kur'ani A Talabijin Na Uganda

21:00 - July 18, 2017
Lambar Labari: 3481712
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shirin kur'ani mai tsarki a gidan talabijin na kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, Ali Bakhtiyari shugaban ofishin yada al'adun muslunci na Iran a Uganda shi ne ya jagoranci shirin.

Shi am a nasa bangaren Muhammad Hussain Hashimi mataimakin shugaban karamin ofishin yada al'adun muslunci ya kasance daga ikin wadanda suka bayar da gudnmawa domin samun nasarar shirin.

Ya kuma bayyana cewa yana daga cikin abubuwan da bangaren kula da al'adun muslunci a ma'aikatar harkokin wajen Iran ke mayar da hankalia kansa a kasashen musulmi.

3620067



An Fara Watsa Shirin Kur'ani A Talabijin Na Uganda

captcha