Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto daga shafin i24news cewa, sojojin yahudawan haramtacciyar
kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus mako daya bayan hana
palasdinawa yin salla a masallacin kudus mai alfarma
Tun da safiyar yau ne sojojin yahudawan su ka kafa shinge na karfe a kofar Babul Asbat ta masallacin kudus, kamar kuma yadda su ka mamaye duk wasu hanyoyin da su ke isa zuwa ga masallacin.
Rahotanni daga kudus sun cewa; 'yan sahayoniyar sun girke sojoji dubu sha biyar a cikin birnin na Kudus.
Dubban palasdinawa da su ka ki amincewa da su bi ta cikin kofar bincike da 'yan sahayoniyar su ka kafa a bakin masallacin kudus.
A wasu sassa-sassa daban-daban na palasdinu an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin sahayoniya.