IQNA

Ya ubangiji ka salati ga manzon rahmarka Kalmar haskenka, kuma ka cika zuciyata da hasken sakankancewa
Ya ubangiji ka salati ga manzon rahmarka Kalmar haskenka, kuma ka cika zuciyata da hasken sakankancewa.
Ka cika kirjina da hasken iamni
Ka cika tunanina da yin komai bisa sahihin tafarki
Ka cika kudirina da hasken ilimi
Ka cika karfina da hasken aiki
Ka cika harshena da hasken gaskiya
Ka cika addinina da mazhabata da da haske maras iyaka daga gare ka
Ka cika jina da hasken kyawawan abubuwa da hikima
Ka cika kaunata da hasken son Muhammad  da iyalansa aminci ya tabbata a gare su
Mafatihul Jinan, ziyarat Al Yasin 

Wani Bangare Na Karshen Addu'ar Al Yasin