IQNA

Za A Bude Cibiyar Al'adun Musulunci Ta Duniya A Masar

21:41 - August 03, 2017
Lambar Labari: 3481763
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Masar ta sanar da cewa za a bude wata babbar cibiyar al'adun muslunci ta duniya a garin Al-salam na sharm el-sheikh.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin vetogate.com ya bayar da rahoton cewa, wanann cibiya za a bude tane tare da hadin gwiwa da mahukunta a lardin Sinai, da kuma majalisar dokokin kasar.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, bude cibiyar zai zo ne a daidai lokacin da za akaddamar da tsibirin Sinai a matsayin cibiyar yawon bude ta musulmi.

Muhammad Mukratr Juma'a ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar ta Masar ya bayyana cewa, babbar manufar wannan shiri itace bunkasa al'dun muslunci a tsakanin al'ummomin duniya, musamman ganin cewa birnin sharm el-sheikh wuri ne na haduwar al'ummomi daga koina cikin fadin duniya.

Ya kara da cewa, wanann cibiya za yi iyakacin kokarinta domin isar da sakon zaman lafiya da aminci da kuma rahma da addinin muslunci yake dauke da shi zuwa ga sauran al'ummomi na duniya.

Haka nan kuma akwai shiri na horar da wasu daga cikin wadanda za su jagoranci cibiyar kan yadda za su gudanar da aikinsu, inda za a koyar da su yarukan Ingilishi, Faransanci, Jamusanci da kuam Spaniyanci.

Kamar yadda kuma daya daga cikin ayyukansu shi ne har da koyar da harshen larabci ga masu bukata daga cikin masu yawon bude ido a wannan wuri.

3626296


captcha