IQNA

An Hana Kai wa Musulmi Abinci Da Magunguna A Myanmar

21:23 - August 07, 2017
Lambar Labari: 3481776
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron gwamnatin kasar Myanmar tare da wasu masu tsatsauran ra'ayin addinin Buda, sun hana shigar da abinci da magunguna a garin musulmi na Ratidayon da ke cikin lardin Rakhin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan News Agency ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron gwamnatin Myanmar tare da wasu masu tsatsauran ra'ayin addinin buda, sun killace garin Ratidayon, tare da rufe dukkanin hanyoyi hudu na shiga garin, da nufin hana shigar da kayan abinci da magunguna da sauran kayan bukatar rayuwa ga musulmi mazauna garin.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin kare hakkin bil adama na majlalisar dinkin duniya ya zargi jami'an tsaron gwamnatin kasar ta Myanmar da cin zarafin musulmi da kuma yi musu kisan kiyashi.

A jiya ne kwamitin bincike da gwamnatin ta Myanmar ta kafa kan zargin jami'an tsaro da cin zarafin musulmi ya fitar da sakamakon bincikensa, inda ya kore dukkanin rahotannin da kwamitin kare hakkin bil adama na majlaisar dinkin duniya da kungiyoyi are hakkin bil adama na kasa da kasa suka bayar, kan ta'asar da jami'an tsaron kasar gami da 'yan addinin Buda suke tafkawa akan musulmi 'yan kabilar Rohingya, tare da bayyana cewa jami'an tsaron kasar suna gudanar da aikinsu ne bisa doka.

3627373


captcha