Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AA cewa, a cikin watan Satumban shekara ta 2015 ce dai aka bude wannan babban wurin adana kayan tarihi na kur’ani a birnin madina.
Hamza Musa Adam shi ne babban darakta mai kula da wannan wuri ya bayyana cewa, tun daga lokacin da aka kaddamar da wannan wuri, ya zuwa yanzu an samu kwafin kur’anai da aka tarjama acikin harsuna 13 na duniya da suke a wannan wuri.
Baya ga haka kuma akwai kur’anai da aka rubuta su tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke matsayin abubuwan masu matukar muhimmanci na tarihi a wannan kasa, wanda aka nuna su a wannan wuri a lokacin aikin hajji.
Shekarar bana dai ita ce shekara ta biyu da ake nuna wadannan kur’anai na tarihi, da suka hada har da wani kur’anin da aka rubuta tun a shekara ta 488 bayan hijiran manzon Allah, wanda ake adana shi a wannan wuri.
Ya kara da cewa tun daga bude wuri ya zuwa yanzu kimanin mutane miliyan biyu ne suka shiga wurin domin ganewa idanunsu abubuwan da aka tanada na tarihi da suka danganci kur’ani mai tsarki.