IQNA

Diplomasiyyar Iran Wajen Yada Kur’ani A Tsakanin Kiristocin Afirka Ta Kudu

23:39 - August 12, 2017
Lambar Labari: 3481789
Bangaren kasa da kasa, shugaban ofishin yada al’adun muslucni an Iran a kasar Afirka ta kudu ya bayyana irin ayyukan da suke gudanarwa wajen yada manufofin kur’ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin hulda da jama’a na cibiyar al’adu ta jamhuriyar muslunci cewa, a zantawar da ya yi da tashar talabijin ta Rasad, Shahruz Fallagpisheh shugaban ofishin yada al’adun muslucni an Iran a kasar Afirka ta kudu ya yi bayani dalla-dalla kan ayyukan da suke gudanarwa wajen yada manufofin kur’ani a kasar ta Afirka ta kudu.

Ya ci gaba da cewa, bisa la’akari da cewa kasar Afirka ta kudu mabiy addinin kirista ne suka fi yawa akasar, sukan mayar da hankali ne wajen bayyana manufofin kur’ani ga dukkanin bangarori na musulmi da kirista, amma sukan yi la’akari da yanayi da kuma inda suke isar da sakon.

Ya kara da cewa a wasu lokuta sukan ziyarci majami’oi na mabiya addinin kirista, tare da gabatar da shirye-shrye da suka danganci kara wa juna sani kan koyarwar littafan da aka saukar daga sama, inda sukan yi amfani da wannan damar wajen bayyana abububuwan da kur’ani ya mabata kan Maryam (AS) da kuma annabi Isa (AS) da kuma matsayinsu a cikin a ddinin msulunci.

A bangaren msulmi kuma sukan shirya taruka na bayar da horo kan kur’ani da kuma wasu abubuwa da suka shafi addinin muslunci na Karin ilmantarwa.

3629300


captcha