Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin thestar cewa, mahukuntan na Canada sun sanar da daukar wannan mataki ne makonni biyu kafin yin hutun shekara.
Bangaren kula da makarantuna ma’aikatar ilimi a birnin ya sanar da cewa, an dauki wannan mataki ne saboda rashin biyan malaman makarantar albashi, wanda hakan yasa ala tilas a rufe ta saboda gazawa.
Wannan mataki dai ya zo ma malaman makarantar da mamaki da kuma iyayen yara, domin kuwa babu wanda ya bukaci a rufe makarantar hatta su kansu malaman, kuma sun karyata batun cewa baa biyansu albashi, korafi guda ne kawai suka gabatar na cewa albashinsu yay i kadan, suna neman a kara musu albashi.
Mahukuntan na Canada dai sun ce an rufe bangaren sakandare ne kawai na makarantar, amma bangaren firame na nan kuma za aci gaba da karatu kamar yadda aka saba.
Wanann dai ita makaranta mafi jimawa da musulmi da musulmi suke da ita a cikin birnin Toronto, wandda ta hada firamre da sakandare.