Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai Briburt cewa, jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta sake yin wani rubutu na izgili ga addinin musulunci dangane da harin birnin Barcelona.
Jaridar a fitowarta ta ranar Laraba da ta gabata ta buga wani zanen hoto da ke nuna harin ta’addancin Barcelona, a kansa kuma ta rubuta cewa lallai addinin muslucni addinin sulahu da zaman lafiya ne a cikin izgili.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da wannan jarida take cin zarafin addinin muslunci da ma sauran addinai, bisa hujjar fadar albarkacin baki.
A lokutan baya ma ta sha buga zane-zanen batunci da kalmomin izgili ga annabawan Allah, da suka hada har da annabi Isa (AS) da kuma manzon Allah (SAW).
A cikin shekarar da ta gabata ce wasu suka kai hari a kan babban ofishin jaridar a cikin Paris na kasar Faransa inda suka kasha wasu daga cikin ma’aikatan jaridar.