Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na shafaqana yace, , sakamakon sabon rikicin da ya sake kunno kai a yankin Rakhin na kasar Myamnar, dubban musulmi 'yan kabilar Rohingya sun sake barin yankin, inda wasu daga cikinsu suka tsallaka a cikin kasar Bangaladesh.
Rahoton ya ce mahukuntan kasar ta Bangaladesh ta kame wasu daga cikin musulmin tare da tilasta su komawa a cikin kasar ta Myanmar, inda rayuwarsu ke fuskantar barazana.
Mahukuntan Mayanmar dai sun ce rikicin baya-bayan na Rakhin ya balle ne bayan da wasu masu dauke da makamai suka kaddamar da farmaki a kan wasu cibiyoyin tsaro 30 a yankin, tare da kashe jami'an tsaro 12, yayin da su kum asuka kashe 'yan bindiga 80 a cewar gwamnatin kasar ta Myanmar.