IQNA

Shirin Isra’ila Na Gina Sabbin Matsugunnan Yahudawa A Birnin Quds

23:50 - August 29, 2017
Lambar Labari: 3481843
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila na da shirin gina wata sabwar unguwa ta yahudawa a cikin yankunan palastinawa da ta mamaye a cikin birnin qharmuds.

Kamfanin dillancin labaran Palastine Yaum ya bayar da rahoton cewa, ministan tsaron cikin gida na Isra’ila Gilad Ardan tare da wasu jami’ai sun yi wani rangadi a cikin birnin Quds domin duba yadda za a fara aiwatar da wanann shirin.

Tashar talabijin ta bakwai ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, babbar manufar wananns hiri ita ce gina wasu sabbin matsugunnai na musamman a wasu yankuna da ke cikin birnin Auds, wadada za a kebance su ga jami’an tsaro kawai.

Wannan dai yana da cikin shirin da Isra’ila take da shin a tabbatar da cewa ta mamaye birnin Quds baki daya, tare da mayar da Palastinawa saniyar ware a cikin birnin mai tsohon tarihi.

Tuni Isra’ila ta fara daukar matakai na ganin ta kara fadada matsugunnan yahudawa har a cikin yankunan gabashin Quds wanda mazauna yankunan Palastinawa ne zalla. Kamar yadda a halin yanzu an kafa shingayen tsaro a dukkanin yankuna da tituna na birnin har da manyan titunan da ke gefenm masallacin aqsa mai alfarma.

3635781


captcha