IQNA

An Yi Sallar Idi A Masallacin Aqsa

23:35 - September 01, 2017
Lambar Labari: 3481855
Bangaren kasa da kasa, Al'ummar Musulmi Na Gudanar Da Sallar Idin layya a mafi yawan kasashen duniya, tare da gudanar da shagulgulan sallah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Rahotanni daga mafi yawan kasashen musulmi a duniya na bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bukukuwan sallah.

A birnin Quds ma dubban daruruwan musulmi Palastinawa ne suka gudanar da salla a cikin masallacin Aqsa mai alfarma, duk kuwa da irin tsauraran matakan da jami'an tsaron yahudawan Isra'ila suka dauka.

Kamar yadda a yau ne aka gudanar da wannan salla a kasashen nahiyar asia da kasashen turai da mafi yawan kasashe.

Babbar salla a matsayin babban idi da musulmi suke gudanar da layya, kamar yadda kuma masu gudanar da aikin hajji suke yanka hadaya a wannan lokaci.

A wannan karon dai ba a samu sabani a tsakanin kasashen musulmi kamar yadda aka saba samu a lokutan gudanar da bukukuwan sallar idi.

3636916


captcha