Daya daga cikin yankunan da musulmi suke bin wannan hanya domin koyar da kur'ani shi ne yankun Kousseri, inda dubban dalibai kan sauke kur'ani wasu ma sukan hardace duk ta wannan hanya.
Sidqi Muhammad daya ne daga cikin malaman da suke koyar da kur'ani mai tsarki a wannan yanki, ya bayyana cewa suna yin wannan karatu tun kuruciyarsa a shekara ta 1960, inda aka yaye dubban daliban kur'ani mai tsarki ta wannan hanya.
Karatun allo dai ya samo asali ne daga kasashen larabawan arewacin nahiyar Afirka, inda daga bisani kuma shigo kasashen yammacin nahiyar Afirka, wadanda suke hulda ta kasuwanci da kasashen larabawan arewacin Afirka a lokaci, wanda kuma hakan ya yi msuu tasiri matuka har suka karbi muslunci ta hanyar su.
Kasar kamaru tana mutane kimanin miliya 20, kasha 40 cikin dari suna bin addinin gargajiya, wasu 40 kuma kiristoci ne, sai kuma kasha 20 su ne musulmi.