IQNA

Adadin ‘Yan Gudun Hijira Na Musulmin Rohingya Ya Kai Dubu 300

23:41 - September 10, 2017
Lambar Labari: 3481883
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, akwai bukatar taimakon gagawa ga ‘yan kabilar Rohingya da suke yin hijira zuwa Bangaladesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na reuters cewam, babban jami’in majalisar dinkin duniya mai kula da ‘yan gudun hijira ya bayyana cewa, adadin musulmin Rohingya da suke yin gudun hijira daga Myanmar zuwa Bangaladesh ya kai dubu 300 na halin yanzu.

Ya ce ko shakka babu a halin yanzu abin da yake a hannunsu ba zai isa su taimaka musu ba, saboda haka an abukatar taimakon gagawa daga kasashen duniya domin tallafawa wadannan bayin Allah.

Kasar Myanmar dai ta dauki matakin yin kisan kiyashia kan musulmi ‘yan kabilar Rohingya ne bisa dalilin cewa sub a ‘yan asalin kasar ne ba, saboda haka ba za a taba basu damar zama ‘yan kasa ba.

Baya ga kisan kiyashin da aka yi kansu alokutan baya, a cikin ‘yan makonnin ma an kasha dubbai daga cikinsu, tare da kone gidaje da kaddarorinsu, inda sojojin gwamnatin kasar tare da ‘yan addinin buda ne suke yin hakan.

3640186


captcha