IQNA

An Rarraba Kayan Tamako Na Iran Ga ‘Yan Gudun Hijira Na Rohingya

22:05 - September 16, 2017
Lambar Labari: 3481901
Bangaren kasa da kasa, an raba kayan agai da Iran ta aike zuwa kasar Bangaladesh domin raba su ga ‘yan gudun hijira na Rohingya da ke zaune a kasar.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, ya zuwa yanzu an raba kayan agai da Iran ta aike zuwa kasar Bangaladesh domin raba su ga musulmin Rohingya ‘yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin kan iyaka da Myanmar.

A yau ne tawagar ta Iran ta isa wannan sansani tare da halartar Ibrahim Rahimpour babban jami’I mai kula da harkokin yanin Asia na kasar Iran, inda aka raba kayan ga wadanda aka tsugunnar a wurin, tare da jin matsalolin da wasu suk usknat domin sanin matakin taimako na gaba.

Haka kuma murtada Salimi shugaban cibiyar Hilal Ahmar na Iran ya halri wurin, kamar yadda shi ma Abbas Wa’izijakadan jamhuriyar muslunci ta Iran ya halarci wurin.

3642628


captcha