Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bayyana shugabar gwamnatin Myanmar da cewa ta mayar da al’ummar kasar tamkar wasu kaddarorinta ba mutane ba.
A cikin wani bayani da ta gabatar a yau, Aung Suu Kyi shugabar gwamnatin Myanmar ta bayyana cewa babu wani abu na cin zarain da yake faruwa a kasarta, mamakon bayyana halin da musulmin Rohingya suke ciki, sai ta yi dirar mikiya a kan musulmin da ake kashewa suna tserewa domin tsira da rayuwarsu, inda ta e ba ta san dailin da yasa suke yin hijira ba.
Shi ma ana bangaren kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya yana kiran Myanmar ta sauya matsaya akan batun gudanar da bincike
Tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce abu ne mai matukar muhimmnaci ta sami damar kutsawa duk cikin wuraren da ake zargin an take hakkin bil'adama.
Tawagar dai tana son shiga cikin gundumar Rakhin ne na musulmin Rohinga domin gudanar da bincike akan kisan kiyashin da aka yi musu.
Tun a cikin dubu biyu da sha biyu ne dai sojojin kasar ta Myanmar suka bude yaki gadan-gadan akan musulmin Rohonga wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane dubu uku daga cikinsu, da kuma tilastawa wasu dubbai zuwa gudun hijira.