IQNA

Shugaban Kasa:

Zamu Ci Gaba Da Kara Inganta Makamanmu Domin Kare Kai

22:07 - September 22, 2017
Lambar Labari: 3481921
Bangaren siyasa, shugaba Rauhani a okacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron makon kare kai ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kara inganta makamanta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran Hassan Rohani ya jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da karkafa aikin sojinta a dukkan fannoni ciki har da na makamai masu linzami.

Dr Rohani na bayyana hakan nea yayin faretin sojojin kasar a nan Tehran, wanda ake kira da ''makon kare kai'' wanda ake gudanarwa a zagayowar ranar kaddamar da yakin Iran-Irak a shekara 1980.

Babban manufar wannan a cewar shugaba Rohani, shi ne daidaita sahu da sauren kasashen yankin irinsu Isra'ila da Saudiyya wadanda ke kashe bilyoyin daloli don sayen makamai daga kasashen yamma musamen Amurka.

Sannan ya kara da cewa Iran zata karfafa aikin sojinta a kasa da sama dana ruwa, da kara karfinta a yankin, wannan kuma ba tare da neman izinin wata kasa a duniya ba.

A yayin faretin, dakarun Iran sun gabatar da wani sabon makami mai linzami da akayi wa lakabi da ''Khoramshahr'' mai cin matsakaicin zango wanda ke iya kai wa nisan kilomita dubu biyu kuma makamin zai iya daukar makamai masu yawa,

Hukumomin Iran sun sanar da cewa suna da karfin fusaha da zasu iya kara karfin makaman su masu linzami wanda aka takaita a yanzu zuwa kilomita dubu biyu sai dai kuma acewarsa ba'ayi su ba don goya masu makaman nukiliya ba.

A yau ashirin da biyu ga watan Satumba ne aka fara bukukuwan makon kare kai a nan Iran don tunawa da ranar da gwamnatin kasar Iraqi ta farwa kasar Iran da yaki a shekara ta 1980 da nufin kifar da Jiririyar gwamnatin musulunci a kasar.

A lokacin dai, wato shekaru 37 da suka gabata Shugaban kasar Iraqi na lokacin ya ce a cikin mako guda zai kwace iko a kasar Iran har da birnin birnin kasar Tehran, ya kumakawo karshen juyin juya halin musulunci wanda bai dade da kafa gwamnati a kasar ba.

A lokacin dai Sadam ya na ganin tallafi da goyon bayanda yake samu daga manya manyan kasashen duniya da kuma na wasu kasashe larabawa, musamman na yankin, zai cimma burinsa kamar yadda ya tsara.

Amma tseyuwar daka wanda mutanen kasar Iran masu kishin addini suka yi ya tsawaita wannan yakin har zuwa shekaru 8 ba tare da sadam Husain ya sami nasara ba.

A cikin wannan makon dai, kamar yadda aka saba a ko wace shekara akan gudanar da bukukuwa daban daban don tunawa da shekarun yakin da kuma nasarorin da mutanen kasar suka samu kan makiyansu. Daga ciki akwai faretin baje kolin sabbi da tsoffin makamai wadanda JMI ta samar da kuma wasannin sojojidaban daban.

3644853


captcha