IQNA

Zaman Makokin Imam Hussain (AS) A Husainiyar Imam Khomeni (Ra)

23:53 - September 27, 2017
Lambar Labari: 3481941
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman farko na makokin Imam Hussain (AS) a husainiyar Imam Khomenei tare da halartar jagoran juyin juya halin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, a daren yau Laraba an gudanar da zaman farko na makokin Imam Hussain (AS) a husainiyar Imam Khomenei tare da halartar jagoran juyin juya halin musulunci da kuma dubban muminai.

Hojjatol Islam Sayyid Ahmad hatami shi ne ya gabatar da jawab a wurin, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da Imam Hussain (AS) babban lamari ne wanda tarihi ba zai manta da shi ba, domin kuwa abin da ya yi shi ne sirrin wanzuwar addinin muslunci bisa hakikanin koyarwar manzon Allah.

A daya bangaren kuma ya yi nuni da cewa, darussan da gwagwamayar Imam Hussain take koyarwa darussa ne wadanda kowane mutu zai iya amfana da su musulmi da ma wanda ba musulmi ba, domin darussa ne na neman ‘yanci da adalaci da karama da kalubalantar kaya domin tabbatar da gaskiya.

Daga karshe Mirza Muhammadi da Arzi sun gabatar da wakoki na juyiyi da tunatar da mutae waki’ar Asura da shahahar iyalan gidan manzon Allah a hannun azzaluman lokacin.

3647481


captcha