Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na alanba news cewa, Marwan Alaridi ya gudanar da wannan aiki na fasaha mai katarwa ne ta hanyar rubuta kur’ani baki dayansa, amma da salon rubutu da zayyana 114 bisa adadin surorin kur’ani mai tsarki.
Wannan aiki mai matukar kima da wannan mutum masani mai fasahar rubuta ya gudanar an ambace da alwan mudawwana, kasantuwar an yi amfani da salon zayyana da ba a taba ganin irinsa atarihin rubutun kur’ani ba.
Wannan aiki ya dauke shi tsawon shekaru goma yana aiwatar da shi, inda ya yi amfani da hanyoyi na musamman wajen tsara zayyanar daidai da surori da kuma yin la’akari da launuka da suka dace a kowane, ta yadda ba za a maimaita sua wani wrin ba.
Wannan salon a zayyana an fara yin amfani da shi ne tun lokacin daular Usmaniya, kuma ya yi amfani da tsarin zayyana iri-iri da ya hada da zayyara farisawa.
Kur’anin Alaridi yana da shafuka 376 da kuma fadi da tsawo 43x57CM, wanda aka yi amfani da takardu masu laushi da aka samar daga auduga, wanda hakan ya kara fito da kyawunsa.