IQNA

Ayatollah Imami Kashani A Hudubar Juma’a:

Idan Babu Dakarun Kare Juyi Babu Juyi / Babu Tattaunawa Kan Karfin Iran

22:47 - October 27, 2017
Lambar Labari: 3482044
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a a Tehran ya bayyana cewa, babbar manufar makiya ta nuna raunana juyin muslunci a Iran ita ce kokarin ganin sun raunana dakarun kare juyin. Haka na kuma ya yi ishara da cewa batun karfin Iran babu batun tattaunawa akansa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na nan birnin tehran Ayatollah ImamI Kashani ya bayyana cewa babu batun tattaunawa game da karfin tsaron Iran.

A yayin da yake khudubar sallar juma'a, Ayatollahi Imami Kashani ya bayyana cewa magabatan kasar Iran za su bi dukkanin hanyoyin da suka ga ya dace domin karfafa matakan tsaron kasar.

Yayin da yake ishara game da ziyarar da piraministan kasar Iraki Haidar Abadi ya kawo kasar Iran tare da ganawarsa da jagoran juyin juya halin musulinci, Ayatollahi Kashani ya bayyana cewa bai kamata ba irakiyawa su aminta da magabatan Amurka, domin duk kasar da ta yarda da Amurka ta durkushe kuma dukkanin mutuncin da take da shi ya rushe.

Yayin da yake taya al'ummar kasar Iraki murna game da nasarorin da suke samu a yaki da 'yan ta'adda, Ayatollahi Imami kashani ya bayyana cewa , malimai, magabata, Sojoji da dakarun sai kai kowannansu ya taka mahimiyar rawa wajen cin wannan nasara.

Har ila yau Ayatollahi Imami Kashani ya bayyana cewa matakin da dakatun juyin juya halin musulinci na kasar Iran suka dauka a fagen yaki da ta'addanci ya daukaka mutunci jumhoriyar musulinci ta Iran a fadin duniya.

3657165


captcha