IQNA

Zaman Tattaunawa Kan Harkokin Ilimin Musulmi A Kenya

21:14 - October 29, 2017
Lambar Labari: 3482049
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zama kan harkokin ilimin musulmi a kasar Kenya tare da sanin hanyoyin bunkasa hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun msulunci na Iran ya habarta cewa, a jiya , an gudanar da wani zama kan bunkasa harkokin ilimin musulmi a kasar Kenya.

Jami'ar Umma ta muslunci ita ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taron na zaman yini guda.

Farfesa Muhammad karama shi ne mataimakin shugaban wanann jami'a, ya bayyana cewa sun shirya wnnan taron, wanda a cewarsa yana da matukar muhimamnci a dukkanin bangarori ga msuulmin kasar.

Babbar manufar taron dai ita ce sanin bangarorin da musulmi suke fuskantar matsaloli a bangaren ilimi da kuma sanin ahnyoyin magance matsalolin.

Kasar dai tan adaga cikin kasashen da mabiya addinin kirista ne suka fi yawa, amma kuma msuulmi suna da karfin fada a ji a cikin harkoi da daman a kasar.

3657620


captcha