Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a taron rufe babban taron kafofin sadarwa da yada labarai da aka gudanar a Iran, an zabi kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna da kumakamfanin dillancin labaran taqri a matsayin kafaofin yada labaran addini a mataki na farko a wannan shekara.
A irin wannan taro da aka gudanar shekaru 3 da suka gabata, a kowace shekara kamfanin dillancin labaran na iqna ne yake daukar wannan lambar yabo.