IQNA

An Rufe Tashar Kur'ani A Tunisia Bisa Hujjar Rashin Lasisi

22:05 - November 04, 2017
Lambar Labari: 3482065
Bangaren kasa da kasa, Hisham Sunusi mamba a kwamitin kula da harkokin sadarwa na kasar Tunisia ya bayyana cewa an rufe tashar radiyon kur'ani ta kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na arabi jaded cewa, a jiya Hisham Sunusi mamba a kwamitin kula da harkokin sadarwa na kasar Tunisia ya bayyana cewa an rufe tashar radiyon kur'ani ta kasar saboda rashin samun lasisi na watsa shirye-shirye.

Ya ci gaba da cewa babbar cibiyar da ke sanya ido a kan harkokin watsa labarai da sadarwa ta kasar ce ta dauki wannan matakin, bayan da aka yi la'akari da wasu lamurra da suka shafi saba doka da wannan take yi.

Babban lamari daga ciki shi ne, rashin samun izini na watsa shirye-shirye, wanda hakan yasan cibiyar ta aike da jami'anta suka kwashe kayan da ke wurin tare da rufe ginin baki daya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, akwai kaidoji wadanda dole ne kowace kafar watsa labarai ko ta sadarwa ta kula da su yadda ya kamata, rashin kiyaye hakan yana matsayin saba doka da za a iya daukar mataki a kan kowace kafa akansa.

Daga karshe ya bayyana cewa saka batun siyasa a cikin lamurra da suka shafi lamarin tashar kur'ani ya sabawa dukkani kaidoji na kasar, kuma wannan tasha bata kiyaye hakan.

3659705


captcha