Wannan taro dai zai samu halartar musulmi da wadanda ba musulmi ba, da nufin yin bayani kan matsayin hijabi a muslunci da kuma falsafarsa.
Salma Ahmad tana daga cikin wadanda suka shirya wannan taro, ta bayyana cewa, hakika yana da tasiri musamman ga wadanda ba musulmi ba, domin kuwa ana yi musu bayani kan matsayin hijabi da amfaninsa a ta fuskoki daban-daban.
Daga ciki kuwa har da bangaren lafiya da kuma matsayinsa a cikin zamantakewa, kamar yadda kuma hakan bai saba wa addinai ba har da na kiristanci wanda shi ne mafi yawan mutanen kasar suke bi.