Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, Farhan Haq kakakin majalisar
dinkin duniya ya bayyana cewa, halin da kananan yara Palastinawa suke ciki a
kurkukun Isra'ila yana da ban takaici.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai kananan yara fiye da 500 a cikin gidajen kason Isra'ila da suke rayuwa a cikin mawuyacin halin.
Ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta girmama dokokin duniya, ta daina kama kananan yara tana tsare a gidajen kurkuku a matsayin fursunoni, domin hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya, kuma ta gaggauta sakin wadanda take tsare da su.