Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na kafil ya habarta cewa, kamar kowace a wannan shekara ma an gudanar da tarukan arbaeen a cikin nasara, inda miliyoyin masoya Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suka taru.
Daga cikin kasashen da masu ziyara suka zo sun hada da ran, Oman, Kuwait, Bahrain, Pakistan da sauransu, inda suka raya wannan zyara ta arbaeen a wannan wuri mai tsarki, tare da saran miliyoyin al’ummar Iraki.