Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na hqmi.org.sa ya bayar da rahoton cewa, kasashe 20 ne suka samu wakilci a gasar hardar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Tanzania a cikin wannan mako.
Bayanin ya cean shirya gudanar da wannan gasa ne da nufin kara yada lamarin kur’ani mai tsarki da kuma karfafa gwiwa matasa kan sha’anin kur’ani mai tsarki.
Ali Hassan Muni tsohon shugaban kasar Tanzani, da kuma Abubakar bin Zubair bin Ali babban mai bayar da fatawa na kasar, gami da jakadun kasashen larabawa da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi, suna daga cikin wadanda suka halarci taron rufe gasar.
A yayin gudanar da taron kammala wannan gasa an gabatar da jawabai kan muhimamancin raya lamarin kur’ani mai tsarki, da kuma yada sahihiyar koyarwarsa.
Daga karshe an bayar da yautuka ga wada suka halarci gasar, da kuma kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna wazo.
Haka nan kuma an bayar da wasu kyautuka na hidima ga kur’ani ga Abdullah bisfar shugaban cibiyar hardar kur’ani ta duniya, da kuma tsohon shugaban kasar.