Kamfanin dillancin labaran iqna ya
bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na Alsharq ya habarta cewa, Muslim
Saqa Amini shi ne shugaban cibiyar yada al’adu a kasar Qatar ya bayyana cewa,
cibiyar tasu ta shirya wannan baje kolin littafai mafi grma a kasar ne domin
baj littafai mafi jimawa da cibiyar tak mallaka.
Ya ci gaba da cewa daga cikin littafai masu kima da aka nuna a wannan baje koli, akwai kur’ani da aka rubuta tun tsawon shkaru 400 da suka gabata, wanda kimarsa ta kai riyal miliyan 3 na kasar Qatar.
Baya ga haka kuma awai wani kwafin littafn Linjila wanda shi ma ya kai kimanin shekaru 700 da yake a hannun cibiyar, wanda shi ma an nuna shi a wannan baje babban baje koli na kasa da kasa.
Akwai cibiyoyin buga littfai 355 da suka hada da na ciki da waje da suke halatar wannan baje koli, wadada suma sun kawo nasu ittafai.