IQNA

Shiri NaDomin Bayyana Koyarwar Muslunci Ga Al'ummomin Duniya

16:57 - December 03, 2017
Lambar Labari: 3482163
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar da fatawa a kasar Masar ta sanar da wani yunkurin da take na kafa wani shiri domin wayar da kan al'ummomin duniya dangane da muslunci.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, cibiyar bayar da fatawa a kasar Masar ta sanar da wani yunkurin da take na kafa wani shiri domin wayar da kan al'ummomin duniya dangane da muslunci da kuma koyarwar manzon Allah (SAW).

Wannan shirin zai mayar da hankali wajen bayyana matsayin addinin muslucni dangane da lamurra da dama da suka shafi rayuwar zamantakewar jama'a da kuma yadda muslunci yake warware matsaloli da dama a wannan fuska.

Bayanin ya ce malamai da masana za su rika gabatar da kasidu da kuma makalolin da suke rubutawa  akan lamurra da daban-daban da suka shafi rayuwar dan adam da kalubalenta da ke tattare da ita da kuma mafita.

Babbar manufar shirin dai it ace fito da hakikan surar addinin muslunci gas u kansu musulmin da kuma wadanda ba musulmi ba, musamman ma ganin irin yadda ake samun karuwar kyamar addinin muslunci yanzu a duniya sakamakon wasu ayyuka da wasu ke aikatawa da sunan wannan addini.

Haka nan kuma shirin zai rika bayyana dabiun manzon Allah da halayensa wadanda su ne mafi kyawawan halaye na 'yan adamataka, kuma su ne hakikanin halayen da addinin muslunci yake koyarwa.

3669218

 

 

captcha