IQNA

23:44 - December 20, 2017
Lambar Labari: 3482217
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin musulmin Najeriya sun nuna fushi dangane da batun hana wata daliba shedar kammala karatun lauya saboda ta saka hijabi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Anatoli cewa, hukumomi a bangaren shari'a sun hana wata daliba musulmi shedar kammala karatun lauya sakamakon saka lullubi da ta yi a wurin taron yaye daliban.

Majalisar malaman addinin muslunci a Najeriya ta nuna damuwa matuka kana bin da ya faru, tare da kiran mahukunta musamman a bangaren ilimi da su dauki matakai na baiwa mabiya addinai hakkokinsu.

Wannan kira ya zo ne bayan da aka hana Amusa Abdussalam Firdausi shiga dakin taron yaye dalibai da suka kammala karatun lauya ne, sakamakon saka lullubi da ta yi a kanta.

Bayanin ya ce ya kamata a yi dubi a kan yadda lamurra suke wakana, domin kuwa ba adalci ba ne abin aka yi, domin sau tari lamurra da dama sukan faru na cin zarafin mutane saboda addininsu musamman mata kuma lamarin yafi faruwa  a makantu.

Tun bayan da labarin Firdausi ya watsu, kafofin yada labarai na duniya sun dauki labarin tare da yada shi, ta yadda mahukunta  abangaren ilimi a Najeriya suka shiga duba wanna lamari duk kuwa da da cewa har aynzu ba a ji ta bakinsu da kuma irin matakin da za su dauka kan lamarin ba.

3674637

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: