IQNA

20:58 - December 21, 2017
Lambar Labari: 3482221
Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin Najeriya za ta bi kadun batun hana wata dalibar jami’a shaidar karatun lauya sakamakon saka lullubi na musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai Anatoli cewa, ‘yan dokokin Najeriya za su bi kadun batun hana wata dalibar jami’a shaidar karatun lauya sakamakon saka lullubi na musulunci  alokacin da ta zo shiga takin taron yaye daibai.

Bayanin ya ci gaba da cewa, majalisar dokokin ta Najeriya ta bukaci wasu kwamitoc da wasu cibiyoyi na shari’a da s bincika mata hakikanin abin da ya faru kan wannan batu.

Hakan dai ya biyo bayan kiran da majlaisar musulmin Najeriya ta yi ne ga bangaren majalisar dokokin kasar, kan su gudanar da sahihin binke kan hakikanin abin da ya faru kuma a dauki mataki.

Majalisar musulmin Najeriya ta baiwa majalisar dokokin w’adin makonni biyu na ta dau mataki, idan kuma ba haka za a gudanar da jerin gwano a dukkanin fadin kasar domin nuna kiyayya da irin wannan cin fuska.

Korar wannan daliba a yayin gudana da taron bikin yaye dalibai saboda ta saka lullubi na muslunci, ya dauki hankulan al’ummomin Najeriya da kafofin yada labarai a wajen kasar.

3674827

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: