IQNA

21:05 - December 21, 2017
Lambar Labari: 3482223
Bangaren kasa da kasa, A yayin da MDD ke shirin yin zama domin tattauna kudurin da Shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila, wakiliyar Amurka a Majalisar ta yi kasashen Duniya barazana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wani sabon abu a tarihin Majalisar dinkin Duniya, wakiliyar Amurka a MDD Nikki Haley, ta gargadi mambobin kungiyar a kan cewa shugaba Trump, ya shaida mata cewa ta bayar da rahoto a kan duk wata kasa da ta juyawa Amurka baya a kan matakin da ta dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar HKI  a taron majalisar da za a yi inda za a kada kuri'a kan batun birnin Kudus a yau Alhamis.

A cikin wani jawabi da ya gabatar, Shugaban na Amurka, ya ce " Naji dadin sakon da Nikki ta isar a Majalisar Dinkin Duniya ga dukkan kasashen da suke karbar taimakon miliyoyin kudin Amurka, amma kuma su ka kada kuri'ar da za ta yi wa ra'ayinu yankan baya. Suna karbar kudinmu sannan kuma suna kin zabar mu, muna kallon irin wadannan kasashe,  Su je kada su zabe mu, mu gaba ta kai mu domin zamu samu damar adana makudan kudade, kuma mu zamu taimaka musu ba.

3674708

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، shugaban amurka ، jawabi ، qudus ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: