Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Morocco News cewa, Daryush yar kasar Morocco ce ‘yar shearu 36 da haihuwa, wadda ta shiga cikin majalisar dokokin dokokin yankin Catalonia.
Haka nan kuma ita ce mace ta farko wadda ta fara shiga wannan majalisa, inda a halin yanzu kuma wasu biyu daga cikin msuulmi sun samu nasara, inda suka zama su uku a halin yanzu.
Wannan yar majalisa musulma ta yi alkawalin cewa daga cikin abubuwan da za ta mayar da hankali kan a majalisa akwai zaman lafiya da sulhu da kuma yaki da tsatsauran ra’ayi.
Haka nan kuma ta sha alwashin kare hakkokin marassa rinjaye a yankin da suka hada har da musulmia cikinsu.
Zaben ‘yan majlaisa dokokin Catalonia karo na sha biyu ya zo ne ‘yan watani ayan kuria’ar raba gardama ta neman ballewa daga kasar spain, inda mafi yawan masu son ballewa ne suka lashe zaben majalisar.
Kimanin musulmi dubu 515 ne suke rayuwa a yankin Catalonia, wato kimanin kashi 15 cikin dari na al’ummar yankin.