IQNA

22:49 - December 28, 2017
Lambar Labari: 3482245
Bangaren kasa da kasa, a cikin watan ramadan mai zuwa n ake sa ran za  afara aiwatar da wani shiri mai taken tafiya zuwa ga kur’ani a Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iidr cewa, a cikin watan ramadan mai zuwa n ake sa ran za  afara aiwatar da wani shiri mai taken tafiya zuwa ga kur’ani a jami’ar queen Merry da ke birnin Lodon na kasar Birtaniya.

Bayanin ya ce shirin zai kunshi horo ne na tsawon wasu kwanak a cikin watan na Ramadan, inda za a koyar da darussa daga cikin surori 114 na kur’ani mai tsarki, wanda kunshi darussa 99 baki daya.

Shirin zai hada da masu halarta kai tsaye a cikin ajujuwa, da kuma wadanda suke bukatar bin shirin daga nesa ta hanyar yanar gizo.

Cibiyar Nazari kan ilmomin kur’ani ta Birtaniya BAQS tare da hadin gwiwa da cibiyar binciken addinin muslunci ta IIDR ne suka dauki nauyin shirya wannan shiri, wanda zai samu halartar malamai da kuma masana kan kur’ani.

3677135

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Birtaniya ، Ramadan ، BAQS ، IIDR ، London ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: