Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sky news cewa, a jiya wasu 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyanci sun yi wa wani matashi yankan rago a garin Alarish dake yankin Sinai na kasar Masar.
Bayanin ya ci gaba da cewa 'yan ta'addan sun kame wannan matashi ne tare da tuhumar cewa yana bin diddigin lamarinsu, wanda hakan yasa suka kafirta tare da yanke masa hukunci kisa.
'yan ta'addan sun fito da shi a bainar jama'a tare da yi masa yankan rago, wanda hakan ya saka tsoro a cikin zukatan jama'a matuka.
Masu dauke da akidar wahabiyanci da ke aiwatar da ayyukan ta'addanci da sunan jihadi a kasar Masar sun addabi al'ummar yankin Sinai, musamman ma tun bayan kashin da suka sha a kasashen siriya da Iraki a hannun dakarun kasashen biyu.