Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, a cikin bayanin da ta fitar cibiyar addinin muslunci ta Azhar da ke kasar Masar ta ware wani bangare na musamman a baje kolin littafai na duniya a Alkahira mai suna Quds da ake gunarwa a karo na arbain da tara.
Haka nan kuma an ba wannan baje koli na shekarar 2018 taken taimakon Quds, inda kasashen duniya talatin da bakwai suke halarta, tare da baje kayayyakin madaba'natu daban-daban na musulunci, da suka hada da littafai da kuma kayan fasaha.
Bayanin ya ci gaba da cewa, cibiyar ta dauki wannan matakin ne bayan taron da ak agudanar a kwanakin baya kan Quds, wanda shi ma ya samu halartar bangarori daban-daban na kasashen musulmi, da nufin kara daura damara domin kare martabar wanann masallaci mai alfarma.
A kwanakin baya ne dai shugaban Amurka ya fito ya shelanta birnin Quds a matsayin babban birnin yahudawan sahyuniya, lamarin ke ci gaba da fuskantar kakkausar martini daga kasashe daban-daban na duniya.