Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dunyal watan cewa, a yau ne za a fara gudanar da babban taron karatun kur'ani mai tsarkia birnin kazablanka na kasar Morocco tare da halartar daruruwan makaranta a fadin kasar baki daya.
Wannan taro dai zai hada da dukkanin bangarori na makaranta kur'ani maza da mata, kamar yadda kuma za a bayar da dam,a ga alkalai domin yin hukunci wajen fitar da makaranta da suka fi sauti dakiyaye abubuwan da ake bukata.
A shekarar da ta gabata an gudanar da wannan gasar ne a matsayin ta kasa da kasa, inda makaranta daga ciki da wajen kasar musamman daga kasashen larabawa da na msuulmi suka halarta, amma a bana 'yan kasar ne kawai sai kuma larabawa da suke zaune a cikin kasar.
Daga karshe za a bayar da kyuatuka na musamman ga mutane goma sha biyu da suka fi nuna kwazo, kamar yadda kuma taron gasar zai ci gaba da gudana daga yau har zuwa tsowon kwanaki hudu a nan gaba.