IQNA

Amurkawa Na Bayar Da Kariya Musulmi Suna Salla A Gangamin Adawa Da Trump

23:13 - January 27, 2018
Lambar Labari: 3482341
Bangaren kasa da kasa, daruruwan Amurkawa ne ad suka hada da musulmi da wadanda ba musulmi suka yi gangamin adawa da Trump a birnin New York.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Hafintong Post cewa, Ch;oe Breyer shugaban cibiyar kula da harkokin addinai ta New York ya bayyana cewa, yadda Amurkawa wadanda ba muuslmi suka bayar da kariya ga muuslmi suna salla, yana fatan hakan ya ci gaba.

Ya ci gaba da cewa ko shkaka babu abin da ya gani abun burgewa, yadda mutane masu addinai da akidu daban-daban suka taru a wuri gudabisa mafufa guda, ita nuna adawa da salon mulkin nuna wariya da kymar wani jinsin ‘yan adam da kuma kymar baki, wanda siyasar gwamnatin Amurka ta ginu a kansa  a halin yanzu.

A jiya ne dai aka gudanar da wannan gagarumin gangami a dandalin Washington square da ke tsakiyar birnin New York, domin nuna rashin amincewa da salon bakin mulki da bakar siyasar shugaban kasar ta Amurka.

3685536

 

 

 

captcha