Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na hubbaren Alawi cewa, wata tawagar malamai da masana daga cibiyar Azhar ta kasar Masar karkashin Walid Matar ta ziyarci hubbaren Imam Ali (AS) da ke Najaf inda suka gana da Muhammad Razuki mai kula da hubbaren mai tsarki.
Walid Matar daya daga cikin manyan malaman cibiyar Azhar da ke jagorantar tawagar ya bayyana cewa, hakika samun damar ziyartar wannan wuri mai tsarki babban dace ne, kuma yana daga cikin abin da suka jima suna fatar samu.
Ya ci gaba da cewa wannan wuri ne da yake dauke hubbarori na manyan bayin Allah musamman Imam Ali (AS) da kuma Imam Hussain (AS) da kuma wasu daga cikin ahlul bait (AS) wanda samun damar ziyararsu babbn dace ne daga Allah wanda ba kowa ne ke samunsa ba.
Kamar yadda ya bayyana farin cikinsa dangane da haduwar da suka yi da wasu daga malaman musulmi na mazhabar shi’ar ahlul bait, tare da kara karfafa dankon zumunci a tsakaninsu.
Al’ummar kasar Masar dai dama an san su da son iyalan gidan manzon Allah, duk kuwa da bayyana akidar wahabiyanci daga bisani a wasu sassa na kasar, amma duk da hakan wannan akidar ta wahabiyanci bata iya buce soyayyar iyalan gidan manzon Allah a cikin zukatan al’ummar Masar ba.