IQNA

Bayani Kan Muslunci A Masallacin Milton Keynes Da Ke Ingila

23:23 - February 01, 2018
Lambar Labari: 3482355
Bangaren kasa da kasa, musulmin birnin Milton Keynes na kasar Birtaniya suna gayyatar kowa masallacinsu domin samun bayani kan muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na miltonkeynes.co.uk cewa, wannan zaman taro zai gudana ne a ranar 18 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, duk da cewa musulmi a sassa na kasar Birtaniya suna gudanar duk da cewa musulmin Birtaniya suna gudanar da irin wadannan taruka a duk shekara, amma a wannan karon zai banbanta da saura.

Al’ummar wannan birni dai suna da kyakyawar fahimta tsakaninsu da musulmi, kuma gudanar da wannan taro zai kara basu damar sanin addinin muslunci ta hanya gabatar da tambayoyinsu.

A ranar 18 ga wannan wata na Fabrairu ne za a gudanar da tarukan bude kofofin masallaci ga dukkanin jama’a musamman ma wadanda ba musulmi ba a fadin kasar Birtaniya.

3687469

 

معرفی اسلام در مسجد میلتون کینز انگلیس/ آماده

معرفی اسلام در مسجد میلتون کینز انگلیس/ آماده

معرفی اسلام در مسجد میلتون کینز انگلیس/ آماده

 

 

 

 

captcha