Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na mir’at Bahrain cewa, a jiya kotun masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta sake yanke hukuncin dauri da kuma kisa a kan ‘ya adawar siyasa da kuma na banbancin akida da suka kai mutane 58 a fadin kasar.
An yanke hukuncin kisa a kan mutane 2, wasu 19 kuma daurin rai da rai, wasu 17 shekaru 15 a gidan kaso, 9 kuma daurin shekaru 10, wasu 11 kuma shekaru 5, yayin da 47 daga cikin an janye musu hakkinsu na zama ‘yan kasa.
Masarautar kama karya ta kasar Bahrain dai ta fara daukar irin wadannan matakai a kan duk wani mai adawa ta siyasa a kasar tun kimanin shekaru bakwai da suka gabata, inda masasautar ta yi amfani da karfi wajen kasha adadi mai yawa na masu neman a gudanar gyare-gyare a cikin tsarin tafiyarwa na kama karya a kasar.
Fiye kashi tamanin da kashi tamanin da biyar cikin dari na mutanen Bahrain dai mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait ne, sauran kuma sun hada da ‘yan sunna da kiristoci da yahudawa, yayin da ‘yan tsraru tsakanin al’ummar kasar su ne wahabiyawa, wadanda turawan mulkin mallaka suka mika musu ragamar tafiyar da kasar.