IQNA

An Jaddada Wajabcin Gurfanar Da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci A Taron Masar

23:40 - February 28, 2018
Lambar Labari: 3482438
Bangaren kasa da kasa, a taron da aka kammala na fada da tsatsauran ra’ayi a mataki da kasa da kasa a Masar, an jaddada wajabcin daukar matakan shar’a kan masu goyon bayan yan ta’adda.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a taron da aka kammala na fada da tsatsauran ra’ayi a mataki da kasa da kasa a Masar, an jaddada wajabcin daukar matakan shar’a kan masu goyon bayan yan ta’adda tare da tallafa musu.

Wannan zaman taro dai an gudanar da shi har na tsawon kwanaki biyu, inda masana daga kasashen duniya 50 suka halarci zaman, tae da gabatar da kasidu da ke bayyana mahangarsu kan batun ta’addanci da kuma yadda za a shawo kansa.

Mafi yawan masu gabatar da jawabai suna danganta ta’addanci ne daga babban tushensa na satsauran ra’ayi da wasu suke dauka daga cikin musulmi tare da kafirta sauran ‘yan uwansu musulmi, kamar yadda a cikin kiristoci ko yahudawa ana samun irinsu.

Dangane da yadda za amagance lamarina cikin kasashen musulmi, masana da suka halarci taron suna ganin yin afani da karfi shi kadai ba zai wadatar ba, domin kuwa ta’addanci akida ce da ake damfara ta da addini.

Ina suke anin dole ne a samar da canji a cikin manhajar karatun addini a makarantu a kasashen da suke bin akidar wahabiyanci, domin asalin akidar kafirta musulmi ta samo asali ne daga wannan akida da wahabiyanci ya ginu a kanta.

3695373

 

 

captcha