IQNA

Amurka Za Ta Ci Gaba Da Taimaka Ma Saudiyya A Yakin Da Take Yi A Yemen

22:42 - March 02, 2018
Lambar Labari: 3482446
Pentagon: Amurka Za Ta Ci Gaba Da Taimaka Ma Saudiyya A Yakin Da Take Yi Da Yemen

Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta sanar da cewa, ci gaba da taimaka ma Saudiyya ayakin da take kaddamarwa kan kasar Yemen wajibi ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, a taron manema labarai da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Dana White ta gudanar, ta bayyana cewa dole ne Amurka ta ci gaba da taimaka ma Saudiyya a yakin da ta kaddamar kan Yemen, domin kare Saudiyya daga hare-haren mayakan Huthi.

Dana White ta ce ayyukan Amurka za su zama kashi biyu ne a Yemen, yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda, sai kuma taimaka ma Saudiyya wajen yaki da masu kai mata hari da ta ce suna samun dauki daga Iran.

Wannan furuci ya zo ne bayan da Amurka da kawayenta Birtaniya ta Faransa suka samun nasara a kan Iran a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, inda suka gabatar da kudiri da ke tuhumar Iran da taimaka mayakan Huthi, ba tare da gabatar da wata hujja da za ta iya tabbatar da hakan ba.

Kafin hakan dai majalisar dinkin duniya ta tabbatar a cikin wani rahoton da babban sakatarenta Antonio Guterres ya gabatar wa kwamitin tsaro, da ke tabbatar da cewa babu wata sahihiyar hujja kan zargin cewa Iran ta baiwa mayakan Huthi makamai.

Baya ga haka kuma majalisar ta fitar da rahotanni masu tarin yawa kan dubban fararen hula da suka rasa rayukansu da suka hada da mata da kanan yara a Yemen sakamakon hare-haren Saudiyya a kasar, baya ga rusa daruruwan masallatai, asibitoci, kasuwanni, ma’aikatu, kamfanoni da gidajen jama’a, tare da jefa al’ummar kasar cikin matsananciyar yunwa sakamakon killace kasar da Saudiyya ke ci gaba da yi, ta sama da kasa da kuma ruwa.

3695996

 

 

captcha