Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun musulunci cewa, an gudanar da wani zaman taron karawa juna sani kan matsayin mace a addinin muskunci da kuma mahangar ma’aiki (SAW) a birnin Abuja fadar mulkin tarayyar Najeriya a jiya.
A yayin gudanar da taron malamai da masana daga jami’oi daban-daban na kasa sun gabatar da kasidu, kan matsayin mace a cikin addinin muslunci da kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.
Haka nan kuma an yi wani kwarya-kwaryan baje kolin kayan fasaha na kasar Iran, musamman ma wadanda aka sana’ata da hannu.