Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Palastine yaum ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ya fitar, jagoran kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Francis ya bayyana matukar takaicinsa dangane da kisan gillar da Isra'ila ta yi wa palastinawa 17 a yankin zirin Gaza, tare da bayyana hakan a matsayin abin yin Allawadai.
Paparoma ya ce yana yin kira ga bangarori na kasa da kasa, da suka kai daukin gaggawa ga al'ummar Gaza, musamman ma wadanda suka samu raunuka, domin ba su taimakon da suke bukata domin samun lafiya.
A gangamin da Palastinawa suka gudanar a ranar Juma'a da ta gabata a kan iyakokin zirin Gaza da yankunasu da Isra'ila ta mamaye, sojojin yahudawan Isra'ila sun buew wutar bindiga a kansu, inda nan take suka kashe mutum 16 tare da jikkata fiye da 1400, kuma Amurka ta hana kwamitin tsaro ya yi Allawadai da hakan.