IQNA

Mashhad Zata Dauki Bakuncin Gasar Kur’ani Ta Duniya Ta Daliban Jami’a

23:53 - April 27, 2018
Lambar Labari: 3482608
Bangaren kur’ani, za a gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta duniya ta daliban jami’a karo na 6 wadda za a gudanar a jami’ar Radhawi da ke birnin Mashhad na kasar Iran.

 

Dr. Sayyid Ali Akbar Shamsiyan shugaban jami’ar Radhawi ya bayyana cewa, wannan gasa za ta gudana ne a  cikin wannan wata mai albarka, kuma  acikin kwanaki tsakiyar watan na sha’aban.

Yanzu haka dai mahalarta gasar sun fara isowa domin shiga gasar wadda zata gudana  akaro na shida, wadda jamhuriyar muslunci ta Iran ke daukar nauyinta.

Wannan gasa ta kebanci daliban jami’a muuslmi ne daga sassa na duniya, inda a wannan karo dalibai 44 ne za su kara a gasar, da suka hada da makaranta 19 da kuma mahardata 25 daa kasashe 35 na duniya, daga nahiyoyin Asia Afirka da kuma turai.

Babbar manufar shirya wannan gasa dai ita ce karfafa matasa dalibai muuslmi da ske aratu a jami’oi kan lamarin kur’ani mai tsarki, domin hakan ya zama wata hanya ta yada ilimin kur’ani da kuma karfafa gwiwar dalibai musulmi.

Gasar dai za ta dauki tsawon kwanaki uku ana gudana da ita, daga karshe kuma za a bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3708640

 

 

captcha